Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya kawo maku cewa: kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta shiga yakin da take da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya tun daga farkon kaddamar da farmakin guguwar Aqsa da nufin tallafawa al'ummar Gaza da ake zalunta da kuma kiyaye tsaro da yankin kasar Labanon a matsayin muhimmin bangare na goyon bayan Gaza. Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tana kai hare-hare da dama a kan arewacin yankunan da Isra’ila ta mamaye a kullum, ta yadda wadannan yankunan na soji suka zama ba kowa.
A tsawon tarihinta na tsiya, gwamnatin Sahayoniya ta kasance da ta gaza a cikin yakin gaba da gaba ta sha kaye to tana fara aikata ta'addancin kisan kai ne. Mummunan tarihin wannan gwamnati yana cike da kai hare-haren ta'addanci iri-iri a sassa daban-daban na duniya.
Don haka a yakin da kungiyar Hizbullah ta yi wa Isra'ila lalas, sai ta fara amfani da gungun kisan gilla kan al'ummar kasar Lebanon da shugabannin kasar, inda Isra'ila ta aikata daya daga cikin manyan laifukan ta’addancin kisa a tarihin dan Adam.
Hare-haren fashewar na’urorin Pagers na wayoyin sadarwa sun jikkata ko kuma kashe dubban mutanen Lebanon cikin kwanaki biyu.
"Shahidi Sayyid Hassan Nasrallah", babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana a cikin wani jawabi bayan wannan laifin ta’addanci; "Makiya sun kai hari kan wayoyin sadarwa na Pagers guda 4,000 a ranar Talata, kuma makiya yahudawan sahyoniya sun nemi kashe mutane 5,000 ta hanyar fashewar sadarwa a jiya Talata. Babban sakataren kungiyar Hizbullah a Labanon ya jaddada cewa kashe-kashen da aka yi a ranakun Talata da Laraba wani laifi ne na yaki da shelanta yaki da kasar Labanon, gwamnatin Isra’ila ta nemi kashe dubban mutane a kasar Lebanon, kuma wannan laifin yana cikin jerin bakin tarihinsu".
Kisan gillar da aka yi wa manyan kwamandojin gwagwarmaya a jere da kuma kisan babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon ya kasance na karshe kuma mafi muni da gwamnatin Sahayoniyya ta yi kan gwagwarmayar da a kasar Labanon. Yanzu, bayan shafe shekara guda ana gudanar da abubuwa masu zafi a Labanon da kuma sauye-sauyen siyasa tare da tsoma bakin Amurka da kasashen yammacin duniya a kasar Labanon domin kawo gwamnatin da za ta kwance damara ko kuma matsa lamba ga gwagwarmayar Hizbullah da ta kasance a raye kuma ta ci gaba da tafiya kan turbar gwagwarmaya amma tare da hakuri bisa dabaru.
Dangane da haka, Zulfiqar Daher mai fafutukar yada labaran kasar Labanon ya rubuta a Al-Manar cewa: watan Satumba na wannan shekara wata ne mai nauyi, tare da wahalhalu da sadaukarwa da a shekarar da ta gabata ta zo da shi, ta yadda manyan jagorori karkashin jagorancin Sayyid Hasan Nasrallah jagoran shahidan al'umma da gungun 'yan'uwa da abokan taFIYA da jagorori da mujahidai wadanda suka tabbatar da Gwagwarmaya da kuma karfafa ta.
Wannan [harin] an fi kaiwa kudanci, da Bekaa da yankunan kudanci, ba tare da barin Beirut, babban birnin kasar da sauran yankuna da dama a arewa da Jabal Lebanon sun zauna lafiya ba. Wanda da farko ya nufi kudanci, da Bekaa da yankunan kudanci.
Duk da wannan sadaukarwa ta gwagwarmaya da al'ummarta sun jajirce kyam wanda aka iya nazarin hakan a tsawon tarihi da fahimtar musabbabi da mahalli da tasirinsa a nan gaba, akwai bukatar yin bincike, bincike da tunani, ba wai kawai kan ci gaba da wannan tsarin gwagwarmaya ba, har ma a kan daidaiton dukkanin yankin musamman kan makomar wanzuwar Isra'ila, wadda ta yi komai amma ta kasa kawar da gwagwarmaya da kuma kasa cimma burinta na manufofin da ta anbata a yakin. Don haka a al'ummar kasar Labanon da gwagwarmaya sune masu nasara da alfahari a wannan yaki kuma ba su mika wuya ga bukatun makiya ba; makiyan da ke ci gaba da kara matsin lamba ta hanyoyi daban-daban tare da goyon bayan muguwar gwamnatin Amurka a fili da kuma tabbatar da abin da ta kasa cimmawa a cikin mummunan zaluncin da take yi wa kasar Labanon.
A wannan watan na Satumba, a daidai lokacin da aka samu sauyi na musamman tare da shahadar Sayyid Hassan Nasrallah a ranar 27 ga wata, kuma ta kasance wani gagarumin sauyi ga iyalan gwagwarmaya da iyalan Sayyid Nasrallah bayan shahadar dansa Hadi a ranar 12 ga wannan wata na shekarar 1997.
A fafatawar Jabal Rafii’, an samu cikakken hadin kai tsakanin mayakan na gwagwarmaya da sojojin kasar Lebanon, inda jinin mayakan ya yi cudanya da jinin ‘yan uwansu sojoji da ke cikin sojojin, kuma wasu gungun shahidai sun shahada tare da Sayyid Hadi, wanda a cikinsu akwai Laftanar Janar Jawad Azar, wanda ya tabbatar da hadin kai tsakanin ‘yan gwagwarmaya da sojoji.
A cikin karrama da girmama wannan aiki, wanda ya gauraya da jini, wato dacewar haduwar ma'auni na "sojoji, gwagwarmaya da kuma al'umma," wanda ake daukarsu a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da ke da iko a kasar ta Labanon, ta fuskacin hadurran da ke kewaye da kasar, kuma a sahun gaba na wadannan hadurran shi ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, amma wasu na kokarin gabatar da wani dubi sabanin hakan.
Dokta Ali Hamieh, wani mai bincike kan al’amuran dabarun siyasa, ya ce game da dukkan wadannan al’amura: “Yawanci, duk lokacin da matsaloli wahalhalu suka tsananta ga gwagwarmaya to takan kara samun karfine, gwagwarmaya ba ta kara girma ko ci gaba sai idan a takurata. Ya yi nuni da cewa, wannan gwagwarmayar wata aba ce ta ke jure abunda sojojin duniya ba za su iya jurewa ba, ba wai kawai ga fuskantar makiya Isra'ila kadai ba, har ma da dukkanin jiragen ruwan yammacin duniya da suke da su, musamman ma jiragen ruwan Amurka. Ya ci gaba da cewa "Har yanzu muna iya yin gwagwarmaya kuma tabbas za mu yi nasara".
Ya kara da cewa: " Gwagwarmaya ta kawar tare da fallasa hanyoyin makiya Isra'ila da na Amurka a duk fadin yankin, abin da ya faru a watan Satumban shekarar 2024 abin ban mamaki ne, saboda kwamandojin gwagwarmaya sun yi shahada, yayin da 'yan gwagwarmayar suka ci gaba da gwabzawa da fafatawa tare da samun nasara". Ya ci gaba da cewa: Makiya Isra'ila sun kaddamar da hare-hare na dubban kilomita daga kasar Siriya ba tare da samuwar gwagwarmaya ba, suna kai hare-hare kan kasashen Larabawa ba tare da gwagwarmaya ba, suna yaki a nan da can suna kuma barazana ga Turkiyya da Masar ba tare da wani martani ba, ya kuma jaddada cewa: " Fagen Gwagwarmaya, tun daga Gaza zuwa Lebanon da Yemen da Iran, Iraki da Siriya, ta tabbatar da ingancinta, karfi da ikonta".
Hamieh ya ce: " Gwagwarmaya ita ce nazari, hanyoyi, koyarwa, imani da ka'ida da ba za a iya cin nasara akanta ba." Ya kara da cewa: "Kamar yadda shahidi Imad Mughniyeh ya ce: Muna yaki ne da ruhinmu da imaninmu ba kawai da makami ba." Ya ci gaba da cewa: "Duk da haka, mun yi yaki da dukkan samuwarmu, da koyarwar ruhi da makamai, kuma mun hana makiya yin gaba a Lebanon".
Ya yi ishara da cewa "makiya Isra'ila sun sami wasu damarmaki a cikin dabaru ta kasa, amma ta fuskar dabarun da basu san su ba... Abokan gaba ba za su iya jure wa yanayin wurin da suke ƙoƙarin mamayewa ba, kama daga yanayin soja da tsaro, ko kuma fuskar Al’umma" ya jaddada cewa "makiya ba makawa ne zasu halaka kuma Gwagwarmaya za ta ci gaba da ƙarfinta".
Hakazalika Hamiyeh ya ce: Mun san cewa makiya Isra'ila suna fargabar wanzuwarsu na tsawon shekaru 80, kuma suna kokarin mayar da ci gabanta zuwa ga mai laifin ta’addanci Netanyahu, wanda yake ganin ya fi tsofaffin sarakunan Isra'ila karfi, kuma ya fi Ben Gurion karfi kuma shine matsayin ma'abucin babbar Isra'ila ta, sai dai kuma hakan ba zai faru ba. Ya ci gaba da cewa: Haka nan Gwagwarmaya za tai ta kara ci gaba, kuma ruhinta da jinin Sayyid Hasan Nasrallah da kwamandojin shahidai tun daga Sayyid Hashem Safiuddin har zuwa dukkan shuwagabannin shahidai su ne masu kariya da karfafa hanyar samun nasara insha Allah. Dukkan shuwagabannin shahidai su ne masu kulawa da ƙarfafa tafarkin nasara insha Allah”.
Kalmomin Karshe
Ci gaba da tafarkin Gwagwarmaya na Hizbullah a kasar Labanon duk kuwa da shahadar jagororinta da kwamandojinta da suka yi shahada karkashin jagorancin shahid Sayyid Hasan Nasrallah, ba wani sabon abu ba ne a tarihin wannan zamani domin kuwa tun kafin juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha fama da irin wadannan fitintinu tsawon shekaru arba'in, ta yadda a farkon shekarun nasarar juyin juya halin Musulunci al'ummar Iran suka shaida shahadar gomman jagororinsu da jami'ai da jami'ansu a tsakiyar yakin da aka kakaba mata.
Don haka magoya bayan Hizbullah wadanda suka yi karatu a mazhabar Sayyid shugaban Gwagwarmaya suna ganin tafarkin daukakarsu ne wajen ci gaba da tafarkin Gwagwarmaya kuma sun fahimci cewa wannan tafarki bai dogara ga mutum ko mutane ba, sai dai ya dogara ne da imani cewa jini zai yi galaba a kan takobi.
Your Comment